Connect with us

News

Majalisar Dattawa ta tsige Sanata Ndume daga kujerarsa ta mai tsawatarwanta.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Majalisar Dattawa ta tsige Sanata Ndume daga kujerarsa ta mai tsawatarwanta.

Sauke Ali Ndume daga kujerar na da nasaba da zargin Gwamnatin Shugaba Tinubu da rashin daukar mataki wajen magace yunwa da ke addabar al’ummar Najeriya.

Gobara Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Iyalan Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi Na Kano

Ndume wanda shi ma dan Jam’iar APC mai mulki ne ya kuma yi zargin cewa Shugaba Kasa Bola Tinubu bai san halin da al’umma ke ciki ba, kuma akwai wadanda suke hana shi ganin jama’a da yin magana a kan al’amara.

A zaman ranar Larba shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya gabatar da kudurin tsige Ndume, wanda kuma yan Jam’iyyar APC suka goyi baya.

A halin da ake ciki majalisar ta maye gurbin Ndume da Sanata Tahir Mungono (Borno ta Arewa) a matsain sabon mai tsawatarwa.

Advertisement

Wata wasikda da uwar Jam’iyyar APC ta aike wa mambobinta a majalisar ta bukaci Sanata Ndume ya fice daga cikinta ya koma duk jam’iyyar adawa da yake sha’awa.

Wasikar na dauke da sa hannun Shugaban APC na Kasa Abdullahi Ganduje, da Sakatare, Barista Ajibola Bashiru.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending