News
Ambaliyar Ruwa Ta Katse Babban Titin Da Ya Haɗe Ƙananan Hukumomi Biyu A Yobe
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wani mamakon ruwan sama da aka yi jihar Yobe da ya haifar da ambaliyar ruwa wacce tayi sanadiyyar katse babban titin Damaturu zuwa ƙananan hukumomin Gujba da Gulani wanda ke kai wa har Biu, Hawul, Shani, Kwaya Kusar da Gombi a jihohin Borno da Adamawa.
Jaridar Blueprint newspaper ta ruwaito cewa Lamarin ya auku ne a safiyar ranar Talata a kasu da ƙauyen Katarko wanda ke tsawon kilomita 20 tsakanin sa da Damaturu, babban birnin jihar.
Wani matafiyi mai suna Mustapha Babagana da ya nufi Biu ya shaida wa manema labaru cewa sai da ya bi ta hanyar Gombe wanda nisan kilomita 380 zuwa inda zai je.
Sannan, ƙananan hukumomi 11 cikin 17 na jihar ba za su iya zuwa Damaturu ba sakamakon rushewar gadoji a hanyoyin Potiskum-Gashua, Damaturu-Dapchi da Damaturu-Buni Yadi.
