News
Atiki Abubakar : Tinubu Na Kokarin Tauye Hakkunan Fararen Hula A Nijeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Kuma Dan takarar Shugabancin Kasa a Shekarar 2023 a Jam’ iyyar PDP Atiku Abubakar, ya bayyana matukar damuwarsa game da abin da ya kira a matsayin cin zarafin ƙungiyoyin fararen hula da masu fafutuka da kafafen yaɗa labarai a ƙarƙashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Cikin wata sanarwa da Atiku ya fitar a shafinsa na X, ya kwatanta irin yanayin da ake fama da shi a halin yanzu da mafi tsananin kwanaki na mulkin kama-karya na sojoji, yana mai nuna fargaba kan yadda gwamnatin ke ƙara tauye haƙƙin jama’a da ƙara dabarunta na tsoratarwa.
Atiku ya ce “Kamen da aka yi wa shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Joe Ajaero misali ne ƙarara na kokarin da gwamnatin ke yi na rufe bakin ƙungiyoyin fararen hula da na ƙwadago.”
“Wannan matakin wani ɓangare ne na fafutukar da gwamnatin ke yi na tsoratar da manyan muryoyin jama’a a Najeriya.” in ji Atiku.
Atiku ya soki batun ƙaruwar barazana ga rayuka da tauye ‘yancin ‘yan jarida.
Ya kuma bayyana matakin DSS na mamaye ofishin SERAP a matsayin cin zarafi ga kimar dimokraɗiyya.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta karkata akalarta daga murkushe ƙungiyoyin farar hula zuwa magance matsalar tsaro da ke addabar ƙasar.
