Connect with us

Business

Gwamnati Ta Haramta Wa Ma’aikatan Asibitin Haƙar ‘Crypto’ A Bakin Aiki.

Published

on

FB IMG 1726759308348
Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Hukumar Gudanarwaar Asibitin Koyarwa na Jihar Gombe da ke Najeriya ta haramta wa ma’aikatan asibitin latsa wayoyinsu suna haƙar kuɗaɗen ‘Crypto’ a daidai lokacin da suke bakin aiki.

Hukumar Gudanarwar Asibitin ta ce, ta lura cewa, wannan sabon salon haƙar kuɗaɗen na Crypto na hana ma’aikatan kula da marasa lafiya.

Advertisement

DA DUMI-DUMI: Gwamnan Kano ya Sauke Dukkanin Shugabannin Riƙon Ƙananan Hukumomin Jihar 44.

Wata sanarwar cikin gida da asibitin ya fitar ta ce, ma’aikatan jinyar na da ƴancin gudanar da wasu ayyuka na daban, amma ba a lokacin da suke bakin aiki ba.

Tuni asibitin ya baza wasu jami’ai da su sanya ido don tabbatar da cewa, ma’aikatan jinyar sun mutunta wannan umarni da aka ba su.

Hukumar Gudanarwar Asibitin ta ce, kula da lafiyar al’umma shi ne babban abin da ta sanya a gaba.

Advertisement

Wannan na zuwa ne a yayin da ɗimbin matasa a Najeriya suka rungumi aikin lallatsa wayoyinsu domin tara kuɗin Crypto ta yanar gizo, yayin da wasu ke caccakar su suna danganta hakan da lalaci.

Kodayake wasu masana na cewa, haƙar kuɗin na Crypto na da muhimmanci duba da cewa, duniyar tana ɗaukar sabuwar alkibila.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *