News
Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mutune 40 A mahaifar Ministan Tsaro
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Yan bindiga masu ɗauke da muggan makamai sun afka garin Janbaƙo cikin Ƙaramar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara.
Maharan sun kai farmakin ne ranar Asabar da dare, kamar yadda mazauna ƙauyen suka shaida wa Premium Times. Sun ce akasarin waɗanda aka arce da su duk mata ne da ƙananan yara.
Janbaƙo ya na da tazarar kilomita 10 tsakanin ƙauyen da Maradun, mahaifar Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle.
An kai wannan mummunan farmaki mako ɗaya bayan mutanen garin sun biya Naira miliyan 10 sun karɓo fansar mutum goma da aka yi garkuwa da su daga garin. Haka dai wasu mazauna garin suka tabbatar.
Wani mai suna Ibrahim Haru ya ce ‘yan bindiga sun yi ta harbin kan-mai-tsautsayi yayin da suka afka cikin garin.
Haru ya ce mafiya yawan waɗanda aka yi garkuwa da su mata ne da ƙananan yara.
Ya ce bayan kai harin a ranar Asabar da dare, washegari yau Lahadi an lissafa an ga babu mutum 40 a cikin ƙauyen.
Ya ce sunan mutumin da aka kashe Malam Isah, sai kuma wani yaro da shi ma aka bindige shi.
Ya ce an bindige su a lokacin da suke gudun tserewa.
A cewar sa, akwai masu gadi, amma hakan bai hana mahara afka wa garin ba.
Maradun da garuruwan kewayen ta sun sha fama da hare-haren ‘yan bindiga. Ko a farkon wannan shekara ta 2024 sai da ‘yan bindiga suka kwarara cikin Maradun, har suka yi yunƙurin sace Hakimin Janbaƙo, Lawali Garba, wanda shi ne Sarkin Kudun Janbaƙo. Kuma ɗa ne ga Sarkin Ƙayan Maradun Garba Tambari.
Maradun nan ce mahaifar Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle. Majiya ta tabbatar wa wakilin mu cewa tun da aka rantsar da Matawalle a matsayin minista, sau ɗaya ya je ganin gida.
“Ya je bayan an rantsar da shi ba da daɗewa ba, ya yi sati ɗaya a Maradun. Bayan ya koma Abuja kuma har yau bai ƙara konawa ba,” inji majiyar mu.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
