News
Dubban Mutane Sun Fito Zanga-zanga A Legas Da Abuja A Ranar Cikar Najeriya Shekaru 64 Da Samun Yancin Kai
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Dubban Mutane Sun Fito Zanga-zanga A Legas Da Abuja A Ranar Cikar Najeriya Shekaru 64 Da Samun Yancin Kai
Sabuwar zanga-zanga ta ɓarke a Jihar Legas kan tsadar rayuwa a Najeriya.
Haka zalika rahotanni da Babban birin Tarayya Abuja na nuni da cea Yansandan Najeriya sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da rashin shugabanci nagari a Abuja da safiyar yau.
Muhimman Bayanai Daga Cikin Jawabin Ranar Samun Yancin Kai Na Shugaba Tinubu
Dandazon matasa ne ɗauke da kwalaye da ƙyallaye ya taru a yankin Utako na tsakiyar babban birnin ƙasar suna yin waƙe-waƙen “yunwa muke ji”, da “a kawo ƙarshen rashin shugabanci nagari”.
Babu ‘yansandan da ke wurin suka fara harba musu barkonon tsohuwa.
Masu zanga-zangar sun tsara nuna ɓacin ransu ne a ranar da ake bikin cika shekara 64 da samun ‘yancin kan Najeriya.