News
RIGIMAR FUBARA DA WIKE TA ƘARA MUNI: Gwamnan Jihar Ribas Siminalaye Fubara Ya Maida Wa Tsohon Gwamnan Ribas Kakkausan Raddi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan Jihar Ribas Siminalaye Fubara ya maida wa tsohon Gwamnan Ribas, ubangidan sa kuma Ministan FCT Abuja Nyesom Wike kakkausan raddi.
Fubara ya yi wa Wike shaguɓen cewa, “idan ka ji garwa na kwaram-kwaram, ta damu mutane da kwaramniya, to ’emti’ ce, ba komai a cikin ta.”
Kotu Ta Yanke Wa Dan Shekara 80 Hukuncin Daurin Shekaru Bakwai A Gidan Yari A Kano
Fubara ya ce duk shirme ya Ihun-ka-banza ne Wike ke yi, da ya ce gwamnatin Fubara ɗin ba ta tsinana komai ba.
“Aikin da gwamnati na ta yi a cikin shekara ɗaya ya wuce aiki da aika-aikar da Wike ya yi a Ribas cikin shekara takwas.”
Ya yi wa Wike raddi ne bayan Wike ya ce shi ne ya bijiro tare da ƙirƙiro aikin ‘Ring Road na Ribas, lokacin da ya ke gwamna.
Wike ya yi iƙirarin a lokacin da yake jawabi a wani taron karrama shi da ƙungiyar ‘yan ƙabilar Ijaw na Jihar Ribas suka shirya, wato Rivers Ijaw People’s Congress.
A ranar Lahadi kwana ɗaya bayan Wike ya yi jawabin, dai Gwamna Fubara ya yi masa raddi, cewa Wike ya ‘shirga ta, ya na buƙatar a yi masa gyara.’
Gwamnan ya yi raddi shi kuma a taron Godiya ga Ubangiji da aka yi a babban Cocin Angalika da ke Fatakwal.
Raddin ya na cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Fubara, Nelson Chukwudi ya aika wa kafafen yaɗa labarai, har da PREMIUM TIMES.
A cikin sanarwar ya bayyana ayyukan biliyoyin nairorin da ya ce Gwamnatin Fubara ta yi, “ciki har da gina asibitin kula da masu taɓin hankali, wanda nan gaba zai yi wa su ‘o’o amfani.”
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
