Connect with us

News

Jami’an Hukumar EFCC Ta Gurfanar Da Wasu ‘Yan Siyasa, Ma’aikatan Kotu, Da Basarake

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Alkaluma daga rumbun tattara bayanai na hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC)  an gurfanar da ‘yan siyasa, ma’aikatan kotu, da wani Basarake a jihar Bauchi daga shekarar 2016 zuwa 2024.

Akwai a kalla mabanbantan tuhume-tuhume guda 20 da suka shafi rukunin wadannan mutane a Jihar Bauchi. Tuhume-tuhumen sun shafi damfara, ha’inci, almundahanar kudi, sata, zamba da sauransu.

Tawagar Super Eagle Ta Makale A  Libya.

Daga cikin wadanda EFCC ta gurfanar akwai ‘yan siyasa ko masu rike da ofishin gwamnati mutum biyar, ma’aikatan shari’a guda biyu da kuma Basarake guda daya.

Sai dai, ya zuwa yanzu, tuhuma 12 ne daga cikin 20 aka kai ga kammala su.

Akwai kararraki guda takwas da har yanzu suna gaban kotu, kamar yadda WikkiTimes ta gano bayan nazarin bayanan da ta samu daga rumbun adana bayanai na EFCC.

Advertisement

A daya daga cikin irin wadannan kararraki akwai na tuhumar tsohon kwamishinan kudi na jihar Bauchi, Garba Dahiru, wanda ake tuhuma da karbar miliyan N214 na yakin Neman zaben jam’iyyar PDP a kakar zaben shekarar 2015.

A cewar EFCC, wadanda ake tuhuma sun karbi adadin kudin da ya zarce wanda doka ta tanada, lamarin da ya sabawa dokar tura kudade. Sai dai, har yanzu karar tana gaban babbar kotun tarayya dake Bauchi bayan wadanda ake tuhuma sun musanta aikata ba daidai ba.

An sace Babur Din Dan Jarida A Gidan Gwamnatin Bauchi

A wata karar ta daban, EFCC ta gurfanar da ma’aikatan hukumar shari’a, Hafizu Dauda da Usman Abdulrahman, bisa zarginsu da karkatar da Babura da aka siya domin rabawa wasu ma’aikata da suke zaman mambobi a kungiyar AUPCTRE da mutanen biyu ke cikin shugabanninta reshen jihar Bauchi.

Har ila yau, EFCC ta gurfanar da Abdulrahman Barau, tsohon shugaban kungiyar manoma ta AAUN reshen jihar Bauchi, bisa zarginsa da karkatar da kudin siyan Babura da za a rabawa mambobin kungiyar bashi. Ana tuhumarsa da wasu shugabannin kungiyar da laifin yankar kudi daga albashin mambobin kungiyar tare da karkatar da su.

Mohammed Uba, Dagacin Wuntin Dada a Bauchi, ya gurfana a gaban kotu bayan ya siyarwa da wani mtum filin da ba nasa ba.

Advertisement

A bangaren kararrakin da aka zartar da hukunci akwai ta Ibrahim Aliyu, mataimakin darekta a ma’aikatar kasa da safayo, wanda ya siyar da filin sarkin Dass, Usman Bilyaminu, dake unguwar BSADP a kan kudi miliyan N1. 1.

Yahaya Ahmed Alfa da Abdullahi Aliyu sun fuskanci hukunci bayan kirkirar takardar mallaka (C of O) da gwamna kadai ke bayarwa tare da kwaikwayon sa hannunsa a damfarar da suka yi na siyarwa da wasu mutane filaye a Bauchi.

Sauran wadanda aka hukunta sun aikata laifuka makamantan irin wadanda aka zayyana da suka shafi zamba, almundahana, karya, cuwa-cuwa da sauransu.

 

 

WIKKI TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending