Connect with us

Entertainment

An Kama Wasu Ƴan TikTok Bisa Zargin Cin Mutuncin Shugaban Kasa

Published

on

An kama wasu ƴan Tiktok bisa zargin cin mutuncin shugaban
Spread the love

An tsare wasu ƴan ƙasar Uganda biyu bisa zargin cin mutuncin shugaba Yoweri Museveni, da uwargidan shugaban ƙasar Janet Museveni da ɗan shugaban ƙasar Gen Muhoozi Kainerugaba a dandalin sada zumunta naTikTok.

Majistare Stella Maris Amabilis ta tasa ƙeyar David Ssengozi mai shekaru 21, wanda aka fi sani da Lucky Choice, da kuma Isaiah Ssekagiri, mai shekaru 28, zuwa gidan yari na Kigo har zuwa ranar Laraba lokacin da za su gurfana a gaban kotu.

Cin Hanci Da Rashawa Shi Ne Silar Rugujewar Wutar Lantarki A Najeriya – Hukumar EFCC

Ana zargin su da kalaman nuna kiyayya da yada munanan bayanai kan dangin shigaban ƙasar da wasu mawaƙan da ke da alaƙa da gwamnatin National Resistance Movement (NRM).

Advertisement

A ranar Litinin da ta gabata, mutanen biyu sun bayyana a gaban kotu inda suka musanta zargin.

An gurfanar da su tare da Julius Tayebwa, mai shekaru 19, wanda tuni aka gurfanar da shi a gaban kotu tare da tsare shi a gidan yari bisa zargin aikaita laifuka iri ɗaya.

 

Advertisement

BBC HAUSA

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *