News
Gwamnatin Tarayya Ta Bai Wani Kamfani Lasisin Gina Matatar Mai A Gombe
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin Najeriya ta bai wa kamfanin Process Design and Development Limited lasisin gina matatar mai mai ƙarfin tace mai ganga 27,000 a kullum da garin arrels Dole-Wure, Akko da ke jihar Gombe.
Kamfanin kula da albarkatun man fetur na ƙasa NMDPRA ne ya bayyana hakan ta shafinsa na X a ranar Alhamis.
Kamfanin Process Design and Development Limited kamfani ne da aka yi masa rajista a Kano mai lamba 487883 a watan Agustan 2023.
Kamfanin NNPC na ƙasa a watan Oktobar 2019 ya sanar da gano man fetur a ruwan da ke Kolmani a yankin Arewa maso gabas na ƙasar nan.
Wannan sh ne waje na farko da aka gano mai a yankin Arewa bakiɗaya bayan lalube da aka yi a saman kogin Benuwai.
Kamfanoni Sterling Global Oil da sabuwar Hukumar Bunƙasa Ayyukan ta Ƙasa da kamfanin mai na ƙasa ne za su kula da haƙo man da ke Kolmani.
Sannan kamfanin NNPC ya ce gano man fetur da iskar gas da aka yi a Gongola zai ja hankalin masu zuba hannun jari tare da samar da ayyukan yi ga mutane da ƙarin kuɗin shiga ga gwamnatin tarayya.
A watan Nuwambar 2022, tsahn shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin haƙo man fetur na farko a yankin Arewa da ke tsakanin iyakar jihohin Bauchi da Gombe.
Wannan na zuwa ne a lokacin da ake cigaba da tada matatun man fetur a kasar nan inda matatar man fetur da ke Fatakwal ta fara aiki baya ga fara aikin matatar mai ta Ɗangote.
NNPC dai ya yi alƙawarin farfaɗo da suran matatun man fetur ɗin domin cigaba da bunƙasa harkar mai da iskar gas a Najeriya.
PREMIUM TIMES
-
Opinion4 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion4 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Jihar Kano Ta Shiga Jerin Jahohi 10 Mafi Tara Kudaden Shiga Na VAT A 2026
