Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Himmatu Wajen Kawar Da Cutar Polio – Kwamared Aminu Abdussalam

Published

on

IMG 20241130 WA0000
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Gwamnatin Jihar Kano ta himmatu wajen kawar da cutar Polio a lungu da sako na jihar.

Mataimakin Gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdussalam ne ya sanar da hakan, a yayin da ya Jagoranci taron Kwamitin karta-kwana kan yaki da cutar Polio, a dakin taro na Africa House dake fadar Gwamnatin Jihar.

Gwamnatin Tarayya Ta Bai Wani Kamfani Lasisin Gina Matatar Mai A Gombe

Kwamared Aminu wanda shine Shugaban Kwamitin karta-kwana kan yaki da cutar ya kara da cewa, Cutar shan inna cuta ce da ke haifar da kazanta da kuma yaduwa cikin sauri ta hanyar kai wa mutane hari, musamman yaran da ba sa warkewa matukar ba’a dauki mataki akan lokaci ba.

Bugu da kari ya ce bincike a Duniyar Musulunchin da aka gudanar a cibiyoyin Kasashen Musulmi ya tabbatar da cewa shan Inna cuta ce ba shafar Aljanu ba, adan haka ya ce ya kamata al’umma su bada hadin kai da goyon baya domin a kawar ita gaba-daya.

A nasa bangaren Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi na biyu, wanda ya sami wakilcin Madakin Kano Alhaji Yusuf Nabahani, yayi kira ga Hakimai, Dagatai da masu Unguwannin dake fadin jihar Kano su bada cikakkiyar gudunmawar su, domin a cimma nasarar da ake bukata.

Advertisement

Da yake nasa jawabin, Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce a halin yanzu jihar ce ke kan gaba wajen kamuwa da cutar shan inna inda take da rahoton cutar har guda 20 cikin guda 60 da aka samu a fadin kasar, mafari kenan da ya ce akwai bukatar hada karfi da karfe wajen ganin an kawar da cutar a jihar.

A karshe Sanarwar da Jami’in yada labaran Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano Ibrahim Abdullahi, ya aiko wa Jaridar INDA RANKA ta ce Kwamishinan ya yaba wa Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, a bisa sahale dukkan abubuwan da ake bukata wajen nasarar shirin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending