Connect with us

News

Mafi Ƙarancin Albashi : Ma’aikatan Hukumar Ruwa A Kano Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani  

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Ma’aikatan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani sakamakon rashin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi.

Advertisement

Shugaban Ƙungiyar Ma’aikatan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano, Kwamared Najib Abdussalam, ya bayyana hakan yayin wata hira da Jaridar NIGERIAN TRACKER.

Babbban Jigo A Jam’iyyar Labour party Ya Sauya Shega Zuwa Jam’iyya Mai Mulki Ta APC

Kwamared Najib ya ce dukkanin hukumomi a Kano sun karɓi sabon mafi ƙarancin albashi , banda ma’aikatan Hukumar Ruwa ta Kano. Saboda haka, sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

Advertisement

Ya ƙara da cewa sun cimma matsaya tare da Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Ahmad Garba Bichi, cewa za a jinkirta biyan albashin har zuwa 20 ga watan Disamba. Amma, sun tashi yau suka ga tsohon tsarin albashi ne aka biya .

Da aka tambaye shi game da kasancewar Hukumar Ruwa ta Kano wata hukuma mai samar da kuɗaɗe, ya ce har yanzu ba a sake nazarin kuɗin ruwa ba, kuma akwai hanyar da gwamnati za ta iya taimakawa wajen biyan su albashi kafin sake nazarin kuɗin ruwa, amma ba a yi hakan ba.

Advertisement

Kwamared Najib ya ƙara da cewa idan har za su jira a biya su sabon albashi daga kuɗaɗen shiga da suka samar, yawancin mazauna Kano ba sa amfani da ruwan da Hukumar Ruwa ta Kano ke samarwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending