News
Bello Turji Da Yaransa Da Ake Zarga Da Ta’addanci Sunki Amsa Laifinsu A Gaban Kotu
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Wasu mutane hudu da ake zargin suna da alaka da fitaccen ‘dan ta’adda’ Bello Turji, sun ki amsa laifin da akeyi musu na zargin ta’addanci da yiwa kasa zagon Kasa.
Jridar Daily Trust ta rawaito wadan da ake zargin sun musunta zargin da ake musu a gaban mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja, lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhume 11 da ake yi musu a ranar Litinin.
Wadanda ake zargin sun hadar da Musa Muhammad Kamarawa da Abubakar Hashimu, a.k.a. Doctor da Samuel Chinedu da Lucky Chukwuma, wanda kuma duka suka musanta zargin da ake musu .
Kamfanin dillancin labarai na Ƙasa (NAN) ya rawaito cewa, da ke tuhumar su uku daga cikinsu, ciki har da Bello Turji sunki amsa laifinsu.
Sai dai jim kadan bayan da magatakardar kotun ta kira karar, wadanda ake kara hudu ne kawai suke gaban kotun.
Daga nan sai mai shari’a Nwite ya tambayi inda Bashir Abdullahi yake, wanda shi ne wanda ake tuhuma na 3 koda mai Shari’a ke tambayar ina cikon mutun na 4 da ake zargi babban lauyan gwamnatin tarayya , ya shaida wa kotun cewa Abdullahi ma yana nan a hannu.
Zai dai lauyan ya nemi izinin kotu data yankemusu hukunci “gaba daya da Abdullahi kuma alkali ya amince da bukatar hakan .
Idan ba’amantaba a ranar 16 ga Disamba ta hannun Abubakar, Daraktan Sashen kararrakin jama’a na gwamnatin tarayya Musa Muhammad Kamarawa; Abubakar Hashimu, a.k.a. Doctor; An gurfanar da Samuel Chinedu da Lucky Chukwuma.
Yayin da ake tuhumar Bashir Abdullahi, Bello Turji, Aminu Muhammad da Sani Lawal, wadanda dukkansu ke tuhumar su a matsayin wadanda ake kara na 3, 6, 7 da 8 bi da bi.
