News
Duk Masu ƙin Biyan Haraji Za Su Danɗana Kuɗarsu A Shekarar 2025 – Gwamnnan Kano

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin Kano ta sha alwashin hukunta duk masu ƙin biyan haraji daga shekarar 2025 a matsayin wani ɓangare na kawo gyara ga ɓangaren haraji a jihar.
Sanarwar hakan na ƙunshe ne cikin wani jawabi da Sanusi Bature Tofa yayi , mai magana da yawun gwamnan Kano, Abba Yusuf, a makon jiya.
A cikin jawabin da shugaban hukumar tattara haraji (KIRS) ta Jihar Kano yayi Dr Zaid ,yace gwamnatin tayi wannan gargaɗi ne domin yunƙurin bunkasar gwamnati na inganta harkokin haraji a jihar.
Abubakar ya ce za a kawo gyaran ne domin inganta harkokin haraji da inganta karɓar haraji da tabbatar da makamantansu.
Ya ce gwamnatin Kano na sa ran tattara haraji da ya kai sama da Naira biliyan 20 a kowanne rubu’i na shekarar 2025.
Shugaban ya ce gwamnan Kano ya kuma kori shugaban kula da tattara harajin tare da naɗa sabbi a ƙoƙarinsa na sake fasalin tsarin haraji a jihar.
Wannan mataki, a cewar sanarwar, zai ƙara inganta ayyukan hukumar wajen tattara haraji a yayin da ake sa ran gwamnan zai gabatar da wani sabon kundi na tattara haraji a jihar a cewar mai magana da yawun gwamnan.
Wannan kundi ana sa ran zai magance ƙara inganta karɓar haraji a shekara ta 2025.
“Wannan zai taimaka wa gwamnatin wajen cika alkawarin da ta ɗaukar wa al’umma a ɓangarori da dama,” in ji Sunusi Bature.
