News
Nan Da Kwana Biyar WhatsApp Za Ta Daina Hawa Wasu Wayoyin Hannu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kamfanin Meta wanda shi ne mallakin dandalin sada zumunta na Facebook da Instagram da WhatsApp ya bayyana cewa daga ranar 1 ga watan Janairun 2025, manhajar WhatsApp za ta daina hawa wasu tsofaffin wayoyin Android kamar yadda kafar yaɗa labarai ta DWAfrica ta ruwaito.
Sannan sanarwar ta ce duk wayoyin iPhone da ke aiki kan iOS 12 su ma manhajar za ta daina hawa wayoyin daga watan Mayun 2025.
Kotu Ta Ja Kunnen Jami,an KAROTA Akan Yanda Suke Gudanar Da Aikinsu
Hakazalika, sanarwar ta ce dukkan wayoyin kamfanonin Samsung da LG da Sony da aka ƙera su shekaru 10 da suka wuce, manhajar ba za ta ƙara hawa kansu ba da sunan aiki.
Mahukunta manhajar sun bayyana cigaban fasaha da ake samu a matsayin dalilin ɗaukar wannan mataki da kuma buƙatar da ke akwai ta mayar da hankali ga wayoyi sabbin ƙira.
Ya kuke ganin wannan mataki kuma ta yaya zai shafe ku?

