Uncategorized
Yan hidimar ƙasa za su fara karɓar sabon alawus na Naira dubu 77 a watan Fabrairu mai kamawa —Shugaban NYSC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Advertisements
Advertisements
Darakta Janar na Hukumar kula da Ƴan Hidimar Kasa (NYSC), Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya bayyana cewa za a fara biyan ‘yan hidimar ƙasa sabon tsarin alawus na Naira dubu 77 a kowane wata daga watan Fabrairun 2025.
Advertisements
Da ya ke jawabi a jiya Alhamis ga ‘yan hidimar kasa na rukunin ‘C’ II na 2024 a Katsina, Ahmed ya tabbatar da cewa tuni an saka karin alawus din a kasafin kudin gwamnatin tarayya na 2025 kuma zai fara aiki da zarar an amince da shi.
Advertisements
Advertisements
Ma’aji Ya Nuna Bacin Rai Kan Aikin Makaranta a Doguwa, Ya Bada Sammacin Dan Kwangilar
“Wannan watan (Janairu) ya riga ya kare, amma da zarar an amince da kasafin kudi, nan da watan gobe (Fabrairu), za a fara biyan ku N77,000 maimakon N33,000 da aka saba biya,” in ji shi.
Advertisements
