Connect with us

Sports

Tsohon Ɗan Wasan Arsenal, Mesut Ozil, Ya Shiga Siyasa a Turkiyya

Published

on

ozil
Spread the love

DAGA MAIMUNA RABIU UMAR

Tsohon tauraron kwallon kafa na Arsenal da Jamus, Mesut Ozil, ya shiga harkar siyasa a ƙasar Turkiyya bayan da aka zaɓe shi a matsayin mamba a kwamitin jam’iyya mai mulki ta AK Party a ƙasar.

An zaɓi Ozil, mai shekaru 36, ne a yayin babban taron jam’iyyar da aka gudanar a birnin Ankara a ranar Asabar, lamarin da ke ƙara tabbatar da kusancinsa da Shugaban ƙasar, Recep Tayyip Erdogan.

Advertisement

An Kama Ɗan Kasuwar Angola Da Hodar Iblis A Filin Jirgin Sama A Kano

Ozil ya fara kusanci da Erdogan ne tun a shekarar 2019, lokacin da ya auri tsohuwar Miss Turkey, Amine Gulse, wanda hakan ya zama ɗaya daga cikin dalilan da suka janyo hankalinsa ga siyasa.

Tsohon ɗan wasan na tsakiya ya buga wasanni 92 a tawagar ƙasar Jamus, inda ya taimaka wa ƙasar lashe Kofin Duniya a shekarar 2014. Haka kuma an zabe shi gwarzon ɗan wasan Jamus har sau biyar a lokacinsa.

Sai dai Ozil ya yi murabus daga bugawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jamus a shekarar 2018 bayan gasar Kofin Duniya, biyo bayan zarge-zargen wariyar launin fata da ya yi wa hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar.

Advertisement

Baya ga harkokin wasanni, Ozil ya shahara wajen tsoma baki a rikice-rikicen duniya, inda ya sha sukar gwamnatin China kan musguna wa musulman Uyghur da kuma nuna goyon baya ga ‘yan Palastinu.

Matakin da ya ɗauka na shiga siyasa na nuni da sabuwar tafiya a rayuwarsa bayan ya yi ritaya daga wasan ƙwallon ƙafa a shekarar 2023.

 

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *