Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Sake Bayar Da Lasisin Buɗe Sabbin Matatun Man Fetur

Published

on

images

 

Hukumar Kula da Albarkatun Mai ta Ƙasa (NMDPRA) ta bayar da sabbin lasisi ga wasu kamfanoni guda uku domin buɗe matatun man fetur a jihohin Abia, Delta, da Edo.

Advertisement

A cewar sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na X, an amince da buɗe Matatar Eghudu a Edo, wadda za ta iya tace ganga 100,000 a kullum. Haka kuma, Matatar MB da ke Delta za ta riƙa tace ganga 30,000 a kullum, yayin da Matatar HIS da ke Abia za ta tace ganga 10,000 kowace rana.

Ƴan Sanda Sun Cafke Hatsabiban Ƴan Bindiga 4 A Kano

Jimillar tacewar da matatun za su riƙa yi idan an kammala su ita ce ganga 140,000 a kullum, wanda ake sa ran zai taimaka wajen rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje.

Advertisement

Shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed, ya bayyana cewa matakan na daga cikin yunƙurin gwamnati na ƙarfafa masana’antar mai da habaka tattalin arzikin ƙasa.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending