News
Tinubu Ya Cutar da Al’ummar Rivers Ta Hanyar Ƙaƙaba Dokar Ta Ɓaci — Atiku
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gaza ɗaukar matakan da suka dace wajen magance rikicin siyasar da ke addabar jihar Rivers.
Atiku ya bayyana cewa, maimakon yin sulhu da warware matsalar cikin lumana, gwamnatin Tinubu ta zabi kakabawa al’ummar jihar dokar ta ɓaci, abin da ya kira cutarwa da tauye haƙƙin ‘yan ƙasa.
Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Gwamnan Rikon Kwarya A Jihar Rivers
Ya ƙara da cewa, wannan mataki na nuna rashin iya jagoranci da gazawar gwamnati wajen yin adalci. Atiku ya bukaci a nemo hanyoyin warware rikicin ta hanyar tattaunawa maimakon amfani da ƙarfin gwamnati.
Tun bayan rikicin siyasar da ya kunno kai a jihar Rivers, an sha samun cece-kuce game da rawar da gwamnatin tarayya ke takawa wajen shawo kan lamarin.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
