Connect with us

News

An Kama Soja Da Ɗan Sanda Bisa Zargin Satar Batiran Jirgin Ƙasa A Kaduna

Published

on

IMG 9174

An kama wani jami’in soja da wani ɗan sanda mai suna Ajiye Joel bisa Zargin sace batirori daga Hukumar Jiragen Ƙasa ta Ƙasa (NRC), tare da wani jami’in hukumar a Jihar Kaduna.

Advertisements
Advertisements

SAHARA REPORTS ta ruwaito cewa dakarun sojojin atisayen ‘Fansan Yamma’ ne suka cafke su a ranar 19 ga watan Maris. Wannan runduna ta musamman an kafa ta ne domin yaki da ayyukan ta’addanci a Arewa maso Yamma.

Advertisements

A halin yanzu, an tsare su a reshen rundunar sojoji dake Kaduna yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

Advertisements
Advertisements

Wannan na zuwa ne bayan wata irin wannan badakala da ta shafi wasu sojoji biyu da aka kora bisa laifin satar wayoyin lantarki a Matatar Dangote, Legas.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending