Connect with us

News

Ramadan: Hankula Sun Karkata Daga Siyan Abincin Buda Baki Zuwa Kayan Sallah

Published

on

sallah

‎Yayin da watan Ramadan ke gab da karewa, hankulan jama’a sun fara karkata daga sayen abinci don buda baki zuwa kayan Sallah, musamman sababbin tufafi ga manya da yara.

Wannan sauyin yanayi ya kara armashi a kasuwanni da wuraren dinkin kaya a Kano, inda shaguna da teloli ke cike da kwastomomi.

Advertisement

‎A ziyarar da jaridar Inda Ranka ta kai kasuwannin Sabon Gari, Wambai, da Kantin Kwari, an ga cunkoson Alumma,inda mutane ke zuba ido kan farashin kayan Sallah.

‎Malama Khadija, kwararriyar mai dinkin kaya, ta ce “Yawancin mutane suna kawo kaya a dinka, amma ba su da isasshen kudi don biyan Kuɗin aikin cikin lokaci. Duk da haka, muna farin ciki da ganin mutane suna shirin bikin Sallah.”

Advertisement

‎Wata matar da ta je siyan tufafi, ta bayyana cewa “Na zo ne domin in sayi sabbin tufafi ga ‘ya’yana. Farashi yana da tsada, amma dole ne a yi shiri domin Sallah.”

‎Haka zalika, wasu teloli sun koka kan matsalar rashin wutar lantarki, wanda ke kawo cikas ga aikin su.

Advertisement

Wani mai dinkin kaya ya ce sun  koma amfani da Sola da janareta saboda yawan katsewar wuta, amma hauhawar farashin man fetur yana kara jefa su cikin matsala.”

‎Duk da kalubalen tattalin arziki, jama’a na ci gaba da shirin kammala sayayya cikin annashuwa da farin ciki yayin da Ramadan ke gab da karewa. Kasuwanni na cike da nishadi, alamar cewa bukin Sallah zai zo cikin walwala.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending