News
Duka Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Ɗan Damben Najeriya A Ghana
Wani dan damben Najeriya, Segun Olanrewaju, ya rasu bayan da ya fadi warwas a yayin da yake karawa da abokin dambensa dan kasar Ghana, Jon Mbanugu, a gasar Ghana Professional Boxing League da aka gudanar ranar Asabar a Bukom Arena.
Bidiyon lamarin da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna yadda Olanrewaju ya fadi ba tare da ya tashi ba a tsakiyar fagen daga. Duk da gaggawar da ma’aikatan kiwon lafiya suka yi don ceto ransa, an tabbatar da mutuwarsa, yana da shekaru 40 da haihuwa.
Yamutsi A Filin Idi: Mutane Biyu Sun Mutu, 20 Sun Jikkata A Gombe
Olanrewaju ya kasance fitaccen dan dambe mai kwarewa, wanda ya fafata a wasanni 24, inda ya samu nasara a 13, kaye 8, da kuma canjaras 3. Ya lashe kambun gasar nauyi ta kasa da kuma ta yammacin Afirka a lokutan baya.
Mutuwarsa ta tayar da hankalin duniya, musamman a cikin tawagar ‘yan damben Najeriya, inda suka bayyana alhinin su tare da jin haushin rashin gwarzon da ya bayar da gudunmawa mai yawa ga wasannin damben Najeriya da yammacin Afirka.
Wannan ba shi ne karo na farko da irin wannan abu ya faru ba, domin kuwa a shekarar 2022, wani ɗan dambe dan Najeriya, Chukwuemeka Igboanugo, ya mutu bayan wani mummunan naushi a hanci a gasar NSF da aka gudanar a jihar Delta.
