Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Sauke Mele Kyari, Ya Naɗa Bashir Ojulari a Matsayin Sabon Shugaban NNPC

Published

on

Ojulari and meme

Shugaban kasa , Bola Ahmed Tinubu, ya sauke Mele Kyari daga shugabancin Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) a wani gagarumin matakin gyaran kamfanin.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Laraba, an bayyana cewa an naɗa Bashir Bayo Ojulari a matsayin sabon shugaban NNPC.

Advertisement

Shugaban Tinubu Ya Kore Mele Kyari Daga Mukamin Shugaban NNPCL

Baya ga hakan, Shugaba Tinubu ya yi garambawul ga kwamitin gudanarwar NNPC mai mutum 11, inda Cif Pius Akinyelure ke jagoranta tun bayan naɗa shi a watan Nuwamba na shekarar 2023. A sabon tsarin, Ahmadu Musa Kida zai jagoranci kwamitin gudanarwar kamfanin.

Mele Kyari ya hau shugabancin NNPC a shekarar 2019, lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, bayan ritayar Maikanti Baru. Wannan sauyin shugabanci na daga cikin matakan da gwamnatin Tinubu ke dauka domin sake fasalin harkokin man fetur a Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending