Connect with us

News

‎Sabuwar Ƙungiyar Ta’addanci Ta Bayyana A Arewa , Sun Kashe Fiye Da Mutane 15 ‎

Published

on

IMG 1874
Spread the love

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja ta tabbatar da ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ta’addanci mai hatsarin gaske, wacce ake kira “Ƙungiyar Mahmuda”. Rahotanni sun tabbatar da cewa ƙungiyar ta kashe fiye da mutane 15 a hare-haren da suka kai a wasu sassan arewacin Najeriya, musamman a jihar Neja.

‎Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya bayyana a ranar Juma’a cewa ana zargin ƙungiyar da hannu a hare-haren da suka haɗa da garkuwa da mutane da kashe-kashe a yankunan jihohin Neja da Kwara.

An Kama Mahaifi Da Laifin Jiwa Ɗansa Rauni Saboda Zargin Satar Biskit A Kaduna

‎A cewarsa, shugaban ƙungiyar, wanda aka fi sani da Mallam Mahmuda, na jagorantar ayyukan ta’addanci a yankin ƙaramar hukumar Borgu, inda aka fi fuskantar barazana a ƙauyukan Babana, Dekara da Luma.

Advertisement

‎“Rahotanni sun nuna cewa wata sabuwar ƙungiya da ake zargin tana da alaƙa da ayyukan ta’addanci ƙarƙashin jagorancin Mallam Mahmuda, na kai farmaki da kuma garkuwa da mutane a unguwannin Babana, Dekara da Luma,” in ji DSP Abiodun.

‎Ya ƙara da cewa rundunar ‘yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro domin dakile wannan barazana da kuma kama masu hannu a aikata laifukan.

‎Rundunar ta bukaci al’umma da su ci gaba da bayar da rahotanni da bayanai masu amfani domin taimakawa jami’an tsaro wajen ganin an kawo ƙarshen wannan sabon barazana ga rayuwar jama’a.

Advertisement

 

 

 

Advertisement

SAHARA REPORTS 

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *