Connect with us

News

Ɗalibar Najeriya Ta Maka Shugaban Ƙasar Amurka A Kotu 

Published

on

1745865782287

Wata ɗalibar Najeriya daga Jami’ar Youngstown State, Cynderila Patrick, ta maka Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, a kotu bayan soke bizar karatunta.

Cynderila, mai shekaru 36, ta shigar da ƙarar ne ta hannun lauyanta, Rhys Cartwright-Jones, tana kalubalantar matakin gwamnatin Trump na fatattakar ɗaliban ƙasashen waje, wanda ya shafi soke bizar ta a ranar 8 ga Afrilu.

Xabi Alonso Na Dab Da Ajiye Aiki A Ƙungiyar Bayer Leverkusen, Domin Komawa Horar Da Real Madrid

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Trump na amfani da ƙananan laifuka kamar sabawa dokar hanya wajen soke bizar ɗalibai, musamman a jihar California. Wannan mataki ne da ke haifar da ƙalubale ga ɗalibai da dama masu burin ci gaba da karatu ko aiki a Amurka.

Cynderila, wadda ke zaune a Maryland, ta bayyana cewa tana buƙatar bizar domin samun izinin aiki bayan kammala digirinta a fannin Injiniyancin Sinadarai a shekarar 2024.

Lauyanta ya bukaci kotu da ta tilasta gwamnatin Amurka ta mayar da bizar Cynderila tare da tabbatar da haƙƙinta na samun adalci da damar cika burinta na ilimi da aiki.

 

Advertisement

 

WIKKI TIMES

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending