Business
Bankuna Sun Ƙarawa Kwastomominsu Kuɗin Tura Saƙo Zuwa N6

Wasu daga cikin manyan bankunan Najeriya sun fara cajin Naira 6 wajen aika saƙon SMS ga kwastomominsu, maimakon Naira 4 da ake biya a da.
Wannan canji ya fito fili ne a saƙonnin da bankunan suka aikewa da kwastomomi a safiyar Laraba, kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar.
UTME 2025: JAMB Ta Kama Mutane 40 Da Ake Zargi Da Satar Amsa
Bankunan sun ce ƙarin kuɗin ya biyo bayan tashin farashin sadarwa daga kamfanonin sadarwa a ƙasar.
Duk da haka, Babban Bankin Najeriya (CBN) bai fitar da wata sanarwa kan batun ba. Kwastomomi da dama dai sun bayyana damuwarsu kan yadda bankuna ke ta ƙara kuɗaɗe a kai a kai, lamarin da ke kara musu nauyi a rayuwa.