Connect with us

News

‎Tsoffin Kansilolin APC Sun Yaba Wa Gwamna Abba Kan Biyan Haƙƙoƙinsu

Published

on

b977e08c 6c0d 4f35 aea6 c1c7a345883d

Kungiyar tsoffin kansilolin jam’iyyar APC a Jihar Kano ta kai ziyarar godiya ga Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, bisa kokarin da ya yi wajen ganin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da biyan haƙƙoƙinsu.

‎Tsoffin kansilolin, waɗanda suka fito daga Kananan Hukumomi 44 na jihar, sun bayyana farin cikinsu a yayin taron da aka gudanar a ma’aikatar ranar Alhamis.

Advertisement

An Karkatar Da Sama Da Kashi 70 Cikin 100 Na Kudin Rancen Ɗalibai — ICPC

‎Shugaban kungiyar, Sunusi Kata Madobi, ya ce Gwamna Abba ya nuna ƙauna da jinƙai wajen amincewa da biyan sama da naira biliyan 15 da suke bin gwamnati a matsayin kudin sallama da na ritaya.

‎”Mun gode wa Gwamna Abba bisa wannan karamci. Haka kuma, muna gode wa Kwamishina Waiya bisa jajircewarsa a wannan lamari. Allah ya ba Gwamna Abba damar tazarce a 2027,” inji shi.

Advertisement

‎Kata Madobi ya ce kungiyar tana da mambobi fiye da 3,000 a faɗin jihar kuma za su ci gaba da mara wa gwamnatin Gwamna Abba baya domin ci gaban Kano.

‎A nasa bangaren, Kwamishina Waiya ya nuna godiya bisa ziyarar, inda ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Abba tana bai wa al’umma muhimmanci ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.

Advertisement

‎Ya ce kofa a buɗe take ga duk wanda ke da niyyar mara wa gwamnatin NNPP baya, tare da tabbatar wa tsoffin kansilolin da gwamnati za ta ci gaba da kare walwalarsu.

‎Ana sa ran za a biya kudaden ne a kashi uku a watannin Afrilu, Mayu da Yuni na 2025. Za su shafi kansilolin da suka yi wa’adi tsakanin shekarun 2014-2017, 2018-2020 da 2021-2024.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending