Connect with us

News

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutane Sama da 200 A Zamfara – Inji Ɗan Majalisa

Published

on

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Kaura Namoda/Birnin Magaji a Jihar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya ce ‘yan bindiga sun sace fiye da mutane 200 a yankin mazabarsa cikin makonni biyu da suka gabata.

Yayin wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Laraba, Jaji ya bayyana cewa matsalar tsaro a yankin ta ƙara kamari, inda ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa kafin lamarin ya kazanta fiye da haka.

Advertisement

ASUU Ta Ce Za Ta Maka JAMB Kotu Kan Mummunan Sakamakon UTME

Ya ce a garin Banga kadai, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 60, daga bisani kuma suka kashe 10 daga cikinsu bayan ‘yan uwansu sun kasa biyan kudin fansar Naira miliyan 30 da aka nema.

Hakazalika, wasu mutum 25 sun sake shiga hannun ‘yan bindiga a ƙauyen Gabake, sannan a ranar Talata, aka sake kai hari a ƙauyen Kungurki, inda maharan suka jefa jama’a cikin firgici.

Advertisement

Jaji, wanda ya kasance tsohon Shugaban Kwamitin Tsaro da Leƙen Asiri a Majalisar Wakilai ta 8, ya ce ba zai dace gwamnati ta ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara kaɗai ba, ganin cewa fiye da jihohi 20 ke fama da irin wannan matsala.

“Ina ganin idan za a ayyana dokar ta ɓaci, to kamata ya yi a shimfiɗa ta ga sauran jihohin da ke fama da matsalar tsaro. Wannan ba matsalar Zamfara ba ce kawai, matsalar ƙasa ce. Kuma ba maganar siyasa ba ce, idan ba a tashi tsaye ba yanzu, abin na iya wuce gwamna,” inji shi.

Advertisement

Game da ra’ayoyin da ke cewa a kawo dakarun haya daga ƙasashen waje don yaƙi da ta’addanci a Najeriya, Jaji ya ce bai goyi bayan hakan ba.

“Sojojin Najeriya na da ƙwarewar da za su iya tunkarar ‘yan ta’adda, matuƙar an ba su kayan aiki na zamani da kulawa ta fuskar jin daɗi. Bai kamata mu dogara da dakarun haya ba,” inji shi.

Advertisement

 

 

Advertisement

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending