Connect with us

News

Rahoto: ‘Yan Majalisa Na Cusa Ayyuka Marasa Amfani A Kasafin Kuɗi – BudgIT

Published

on

Wata ƙungiya mai sa ido kan yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati a Najeriya, mai suna BudgIT, ta zargi wasu ‘yan majalisa da cusa ayyuka marasa amfani cikin kasafin kuɗi na shekarar 2025.

A cewar rahoton ƙungiyar, an gano cewa an saka kwangiloli 11,122 a cikin kasafin kuɗin, waɗanda za su lashe kuɗi har Naira tiriliyan 6.93, duk da cewa ayyukan ba su da muhimmanci ko amfani kai tsaye ga rayuwar jama’a.

Advertisement

Jami’an Yan Sanda Sun Bankaɗo Masana’antun Takin Bogi A Bauchi

Wasu daga cikin waɗannan ayyuka sun haɗa da:Raba takin zamani,Bayar da tallafin karatu,Gina cibiyoyin ICT da CBT,Sayen motocin tsaro.

BudgIT ta ce mafi yawan waɗannan ayyuka ba su da alaƙa da ma’aikatun da aka ɗora su a kansu, kuma hakan na nuni da yadda ake karkatar da kasafin kuɗi don biyan buƙatun wasu mutane na kansu.

Advertisement

Ƙungiyar ta ƙara da cewa waɗannan ayyuka marasa amfani sun kai kashi 12.5 cikin 100 na jimillar kasafin kuɗin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi, wanda ya kai Naira tiriliyan 54.99.

Ta ce hakan na rage amfanin kuɗin gwamnati, baya ga ƙara janyo rashin yarda tsakanin jama’a da gwamnati.

Advertisement

BudgIT ta buƙaci gwamnati da ta daina bari a cusa ayyuka marasa amfani a kasafin kuɗi, tare da kiraye-kirayen a riƙa bin gaskiya da adalci wajen tsara kasafi, domin a tabbatar cewa kuɗaɗen gwamnati na amfani da gaske wajen sauƙaƙa wa ‘yan ƙasa rayuwa.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending