Connect with us

News

Sojojin Nijeriya Sun Kashe Ƴan Ta’adda 60 A Bita, Jihar Borno

Published

on

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 101 Sun Kama Wasu 182 A Cikin Mako Daya

Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana cewa dakarunta na Operation Hadin Kai sun kashe ƴan ta’adda akalla 60 a wani farmaki da suka kai a garin Bita da ke ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar da safiyar Juma’a, ta bayyana cewa an kai farmakin ne da haɗin gwiwar dakarun kasa da na sama, inda suka kutsa maboyar ƴan ta’addan tare da musu luguden wuta.

Advertisement

Muhimmancin sada zumunci – Malam Jafar

Duk da cewa rundunar ba ta bayar da cikakken bayani kan yadda harin ya gudana ba, rahotanni daga wani masani a sha’anin tsaro na Yammacin Afirka, Zagazola Makama, sun bayyana cewa harin ya biyo bayan wata arangama ce da ta ɓarke tsakanin ƴan ta’addan da dakarun 26 Task Force Brigade da misalin ƙarfe 1:09 na tsakar dare.

Bayanai sun nuna cewa nan take rundunar sojin sama ta bada goyon baya ta hanyar amfani da jiragen yaki na zamani – A-29 Super Tucano – inda aka fatattaki ‘yan ta’addan cikin gaggawa.

Advertisement

An ce musayar wutar ta ci gaba har zuwa ƙarfe 3:23 na dare, lamarin da ya yi sanadin mutuwar daruruwan ‘yan ta’adda da kuma rusa wasu maboyarsu.

Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar hare-haren ƙungiyar Boko Haram da ISWAP a yankin Arewa maso Gabas, inda cikin makonni kadan suka kai farmaki a sansanin sojoji da ke Marte, tare da kashe dakaru da dama.

Advertisement

Haka kuma, akwai rahotanni na kashe-kashen fararen hula da suka haɗa da manoma da ‘yan kasuwa a wasu sassan jihar Borno, lamarin da ke ƙara tayar da hankalin jama’a.

Rundunar sojin ta bayyana cewa za ta ci gaba da kai farmaki ba kakkautawa domin tabbatar da cewa ba a bar ƴan ta’adda su sake kafa sansani ko tasiri a wani yanki na ƙasar nan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending