Connect with us

News

‘Yan Bindiga Sunyi Ajalin Direbobi Biyu, Sun Ƙone Motocinsu A Imo

Published

on

Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ne sun kai hari kan wasu direbobin manyan motoci a garin Ogi da ke ƙaramar hukumar Okigwe a Jihar Imo, inda suka bindige su har lahira tare da ƙone motocinsu.

DAILY TRUST ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na safiyar Asabar, lamarin da ya tayar da hankula a tsakanin mazauna yankin da matafiya a babban titin.

Sallah Ta Wuce Cikin Lafiya: Babu Cuta, Babu Damuwa – Cewar Gwamnatin Kano

Shugaban ƙungiyar direbobi ta NURTW reshen Okigwe, Dahiru Musa, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya bayyana cewa tuni suka sanar da kwamandan ‘yan sanda (DPO) na yankin domin ɗaukar mataki cikin gaggawa.

“Wasu da ake zargin ‘yan IPOB ne suka tare hanyar suka bude wa direbobin wuta, sannan suka ƙone motocinsu da ke ɗauke da buhunan gari,” inji shi.

A cewarsa, jami’an tsaro sun iso wajen bayan faruwar lamarin, inda suka ɗauki gawawwakin zuwa asibiti kafin daga bisani a yi musu jana’iza.

A nasa bangaren, kakakin direbobi na tashar Laranto da ke Jos, Mahmud Jafaru, ya ce tirelolin da aka kai wa harin na kan hanyarsu ce ta zuwa Fatakwal.

Advertisement

Ya bayyana cewa wadanda suka rasa rayukansu a harin sune Haruna Muhammad da Adamu Ibrahim – direbobi biyu da suka dade suna wannan sana’a ba tare da wani rikici ba.

Mahmud Jafaru ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa domin kawo ƙarshen irin wannan mummunan hali da ke kara yawaita a tsakanin direbobi.

“Yana da muhimmanci gwamnati ta ƙara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin direbobi da sauran matafiya. Saboda abin da ke faruwa yanzu, ba kawai haɗari bane – tsagwaron zalunci ne,” inji shi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending