News
Ambaliya A Mokwa: ‘Yan Majalisa Sun Ce Mutane 600 Da Suka Ɓace Ba Sa Raye
Majalisar Wakilai ta Najeriya ta bayyana cewa mutane fiye da 600 da suka ɓace sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a Mokwa, Jihar Neja, ana kyautata zaton sun mutu.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wani ƙudiri na haɗin gwiwa da ‘yan majalisa daga Jihohin Neja da Kwara — Hon. Joshua Audu Gana da Hon. Saba Ahmed Umaru — suka gabatar a zauren majalisar a zaman da aka gudanar ranar Laraba.
An Kama Manyan Ma’aikatan Asibiti Kan Zargin Ajalin Jarirai Saboda Sakaci
‘Yan majalisar sun ce ambaliyar ruwan, wadda aka samu sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, ta auku ne a ranakun 28 da 29 ga watan da ya gabata, bayan rugujewar tsohuwar gadar jirgin ƙasa da ke Mokwa. Wannan lamari ya haddasa mamayar ruwa zuwa manyan unguwanni da cibiyoyin kasuwanci, ciki har da Tiffin Maza da Anguwan Hausawa.
Hon. Gana ya bayyana cewa “Mutane 500 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da sama da 600 suka ɓace kuma har zuwa yanzu ba a gano su ba. Ganin yadda ambaliyar ta kasance, ana ganin babu wata alama ta cewa suna raye.”
A cewar sa, wannan ibtila’i ya jefa dubban al’umma cikin mummunan hali, inda ambaliya ta rushe gidaje fiye da 4,000, ta jikkata mutane 200, sannan ta lalata gonaki da wasu manyan ababen more rayuwa.
Sun kara da cewa, waɗanda suka tsira daga ibtila’in na cikin haɗarin kamuwa da cututtuka irin su kwalara da zazzaɓin typhoid, saboda gurɓataccen ruwa da rashin tsafta a sansanonin ‘yan gudun hijira da aka girke su.
‘Yan majalisar sun bukaci gaggawar daukar matakin kai dauki daga Gwamnatin Tarayya, Hukumar NEMA da sauran hukumomin jinƙai, don ceto rayukan al’umma da kuma sake farfaɗo da yankunan da ambaliyar ta shafa.
