Connect with us

News

Ayrah Media Concept Ta Jagoranci Tattaunawa Kan Amfanin AI A Harkar Hulɗar Jama’a

Published

on

IMG 20250716 WA0015

A ci gaba da jajircewa wajen haɓaka fannin sadarwa da hulɗar jama’a a Najeriya, kamfanin Ayrah Media Concept ya gudanar da wani babban taron tattaunawa ta yanar gizo a ranar Talata, 16 ga watan Yuli, 2025, domin nuna muhimmancin fasahar Artificial Intelligence (AI) ga aikin hulɗar jama’a.

Taron wanda aka shirya a matsayin gudunmawar kamfanin wajen bikin Ranar Aikin Hulɗar Jama’a ta Duniya, ya gudana ƙarƙashin taken: “Muhimmancin AI a Dabarun Hulɗar Jama’a na Zamani”.

Advertisement

‎Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa Ya Sauya Sheƙa Zuwa ADC

An shirya taron ne tare da haɗin gwiwar Cibiyar Hulɗar Jama’a ta Najeriya (NIPR) reshen Kano, da kuma PrimePulse Communications Ltd.

Masana Sun Yi Bitar Illoli da Fa’idodin AI

Advertisement

Masu ruwa da tsaki daga bangarori daban-daban na ilimi  sun halarci taron, inda suka tattauna yadda fasahar zamani ke sauya yanayin sadarwa, da tasirin da hakan ke da shi ga aikin hulɗar jama’a.

Farfesa Sule Yau Sule na Jami’ar Bayero da ke Kano, ya jaddada cewa lokaci ya yi da NIPR za ta fitar da ƙa’idoji masu tsauri da za su daidaita yadda ake amfani da fasahar AI a cikin aikin hulɗar jama’a.

Advertisement

“AI na iya kwaikwayon saƙon ɗan adam ta yadda ba za ka iya bambancewa ba. Idan ba a kula ba, hakan na iya haddasa yaɗuwar bayanan ƙarya da za su iya lalata amincewa da aikin hulɗar jama’a,” in ji Farfesa Sule.

Ya ce duk da cewa fasahar AI tana da amfani, wajibi ne ƙwararru su rika amfani da ita a hankali da sanin makamar aiki wajen sarrafa bayanai.

Advertisement

A nata bangaren, Dr. Jamila Mohammed Dahiru, malamar jami’a daga Jami’ar Abuja, ta bayyana cewa AI na taka muhimmiyar rawa wajen sauƙaƙa isar da saƙonni ga jama’a musamman a sassan da ke fama da ƙarancin bayanai.

Ta ce shirye-shirye irin su AI Sisters, da kayan aikin zamani kamar chatbots da machine learning, sun taimaka matuƙa wajen ilmantar da mata da matasa a yankunan karkara.

Advertisement

“AI ba zai maye gurbin ɗan adam ba. Sai dai ya zama abokin aiki da zai taimaka wajen ƙarfafa fahimta da gina tausayi da gaskiya a tsakanin al’umma,” in ji Dr. Jamila.

Ayodele Ishola, masani a fannin dabarun sadarwa , ya bayyana cewa amfani da AI wajen gudanar da kamfen da kare kimar kamfani yana da amfani, amma har yanzu sai an haɗa da tunani da ƙwarewar ɗan adam.

Advertisement

“AI fasaha ce mai ƙara wa mutum ƙarfi a isar da saƙo, amma dole ne a yi amfani da hankali ,” in ji shi.

Ya bayyana kayan aikin zamani kamar Top Worker da Prices Guru a matsayin hanyoyi da ake amfani da su wajen inganta saƙonni.

Advertisement

Wani wakili daga Cibiyar NIPR, Mista Aliyu, ya shawarci masu aiki a fannin hulɗar jama’a da su ci gaba da neman ƙwarewa da kuma tabbatar da cewa sun zama mambobi na ƙungiyar domin samun kariya da ci gaba da sanin sabbin dabaru.

A jawabinsa na rufe taron, Auwal Sani, Manajan hulɗar jama’a na Ayrah Media Concept kuma wanda ya jagoranci shirya taron, ya nuna godiya ga mahalarta da abokan haɗin gwiwa.

Advertisement

“Wannan taro wata alama ce ta yadda Ayrah Media Concept ke kokarin zama jagora wajen ƙarfafa tattaunawa kan fasaha da gaskiya a fannin hulɗar jama’a a Najeriya,” in ji shi.

Taron ya bai wa mahalarta damar fahimtar yadda ake amfani da AI ta hanya mai kyau da ƙwarewa, tare da tabbatar da cewa Ayrah Media Concept na daga cikin kamfanonin da ke kan gaba wajen kawo sauyi a harkar sadarwa da hulɗa da jama’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending