News
Jihohi 6 Na Arewa Za Su Kashe Sama Da Naira Biliyan 35 Kan Motoci Da Gidajen Baƙi
Bincike ya nuna cewa akalla jihohi shida daga yankin Arewacin Najeriya sun ware fiye da naira biliyan 35 domin sayen sabbin motoci da gyare-gyaren wasu manyan gine-gine, musamman gidajen gwamnati da wuraren saukar baƙi, a kasafin kuɗinsu na shekarar 2025.
Rahoton da jaridar WIKKITIMES ta wallafa ya bayyana cewa jihohin da suka fi fitar da kuɗaɗe a wannan fanni sun haɗa da Adamawa, Borno, Jigawa, Kebbi, Taraba da Yobe.
Gwamnatin Kano Za Ta Haɗa Gwiwa Da NEPC Don Wayar Da Kan Jama’a Kan Fitar Da Kaya Zuwa Ketare
A Adamawa, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya ware ₦2.9bn domin sayen motoci guda 42, yayin da aka tanadi ₦3.56bn domin gyaran gidajen gwamnati.
Gwamnatin Jihar Borno ƙarƙashin jagorancin Babagana Umara Zulum ta ware ₦6.92bn don sayen motoci da kuma gina sabbin wuraren masauki ga baƙi da ma’aikata.
A Jigawa, an ware ₦1.14bn domin sayen sabbin motoci da gyaran gidan gwamnati da masaukan Kano da Kaduna da kuma gidan mataimakin gwamna.
Haka zalika, Jihar Kebbi ta ware ₦2.36bn don sabbin motoci, sannan ta ware ₦3.3bn domin gyara ofisoshin haɗin gwiwa da ke cikin biranen Abuja, Lagos da Sokoto.
A Taraba, gwamnati ta tanadi ₦2.4bn don gyaran gidan gwamnati da ke Jalingo, yayin da aka ware ₦3bn domin gina sabbin gidajen saukar baƙi a Kakara, Gembu, Takum da wasu yankuna.
Jihar Yobe kuwa ta ware ₦2.18bn domin sayen motocin Hilux guda 30 da Toyota Camry guda 2, tare da tanadin ₦500m domin gina gidan sarki a Damaturu, babban birnin jihar.
Wannan matakin ya haifar da ce-ce-ku-ce da suka daga al’ummomi da kungiyoyin fararen hula waɗanda suka bayyana damuwarsu kan yadda aka ware kuɗaɗen da suka fi dacewa da fannin jin daɗin al’umma kamar kiwon lafiya, ilimi, da kuma tsaro.
Sai dai wasu daga cikin gwamnoni da jami’an gwamnati na bayyana cewa sayen sabbin motoci da gyaran gine-gine na da tasiri ga gudanar da ayyukan yau da kullum da kuma karɓar baƙi yadda ya kamata.
Masana a fannin tattalin arziki da al’amuran yau da kullum sun yi nuni da cewa irin wannan kashe kuɗi kan abubuwan da ba su da tasiri kai tsaye a rayuwar jama’a na ƙara rura rashin amincewa da gwamnati da kuma haifar da gibi tsakanin shugabanni da talakawa.
