News
Ƴan Sanda Sun Kama Ƴan Uwa Da Suka Yi Garkuwa Da Kansu Don Karɓar Miliyoyin Kuɗi A Abuja
Rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja (FCT) ta cafke mutane huɗu, ciki har da ‘yan mata biyu ‘yan uwa, bisa zargin ƙulla shirin bogi na garkuwa da kai da nufin karɓar Naira miliyan biyar daga hannun mahaifinsu.
Mai magana da yawun rundunar, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a ranar Talata, inda ta ce lamarin ya faru ne a unguwar Jikwoyi.
A cewar SP Adeh, ɗiyar mai shekaru 16 ce ta fara da barin gida ranar 18 ga Yuli, inda ta ce tana kan hanyarta ta zuwa rubuta jarabawa a makarantar Government Secondary School da ke Karu. Sai dai daga nan bata dawo gida ba, har sai da mahaifinta, Mista Innocent, ya samu kira daga wasu da ba a san ko su waye ba suna neman kuɗin fansa.
Ƴan sanda sun ce bayan an fara bincike, an gano cewa yarinyar tana zaune lafiya a Jikwoyi Phase II, inda take tare da wasu mutane cikin annashuwa.
Bincike ya bayyana cewa babbar ’yar gidan ce tare da saurayinta suka tsara shirin, kuma ita ’yar karamar ta amince da shiga cikin wannan danyen aiki. An kuma bayyana cewa saurayin, wanda ke da aure, ya taka rawa a wannan makircin.
Babbar ’yar gidan dai ta ci gaba da zama a gida kamar ba ta da masaniya, tana kallon yadda iyayensu ke cikin dimuwa da ƙoƙarin tara kuɗin fansa don kubutar da ‘yar uwarta.
“Mun kama dukkan wadanda ake zargi huɗu, kuma sun amsa laifinsu. Za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike,” in ji SP Adeh.
Kwamishinan ƴan sandan FCT, CP Ajao Adewale, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu matasa ke nuna halin rashin godiya da rashin kunya ga iyayensu, yana mai jan hankalin iyaye su riƙa kula da tarbiyyar ‘ya’yansu da kuma lura da halayensu a gida da waje.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
