Business
Babban Bankin Ghana (BoG) Ya Dakatar Da Lasisin Cinikin Kuɗaɗen Ƙetare Na UBA
Babban Bankin Ghana (BoG) ya dakatar da lasisin cinikin kuɗaɗen ƙetare na bankin UBA reshen ƙasar, na tsawon wata ɗaya daga ranar 18 ga Satumba, 2025.
Wata sanarwa da BoG ta wallafa a shafinta na X ta bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne bisa dokar cinikin kuɗaɗen ƙetare ta shekarar 2006, sakamakon keta ka’idojin kasuwa da bankin ya yi sau da dama.
Babban Bankin Ghana (BoG) Ya Dakatar Da Lasisin Cinikin Kuɗaɗen Ƙetare Na UBA
Sanarwar ta ce UBA Ghana ya gudanar da harkokin tura kuɗaɗe ba tare da izini ba a madadin wasu kamfanonin biyan kuɗi, da suka haɗa da Halges Financial Technologies, Cellulant Limited da Flutterwave Inc., domin kamfanonin tura kuɗi irin su Top Connect, Taptap Send, Remit Choice da Afriex.
Haka kuma, BoG ta sanar da dakatar da duk wata hulɗar haɗin gwiwa tsakanin UBA da kamfanonin biyan kuɗi da tura kuɗaɗe daga ƙetare.
Bankin ya ƙara da cewa ya dakatar da mu’amala da kamfanonin tura kuɗi daga ƙetare irin su Tap Send, Top Connect, Remit Choice, Send App da Afriex, bisa zargin keta ƙa’idojin harkar kuɗaɗen ƙetare a ƙasar.
Kazalika, Babban Bankin ya yi kira ga dukkan kamfanonin da ke cikin kasuwar kuɗaɗen ƙetare na Ghana da su kiyaye ƙa’idojin da aka shimfiɗa, tare da gargaɗin cewa za a ɗauki matakan ladabtarwa kan duk wanda ya bijire wa doka.
