Connect with us

News

Daliba Ta Kare Martabar Jami’ar MAAUN Kan Cece-ku-cen Kuɗin Yaye Dalibai

Published

on

Screenshot 20251202 194538

Wata daliba a Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN), Kano, Fateemah Musa, ta bayyana damuwarta kan yadda ake ta muhawara a kafafen sada zumunta da wasu gidajen jaridu game da kuɗin yaye dalibai na N750,000 da jami’ar ke karɓa.

A rubutun ta, Fateemah ta ce al’amarin da ya kamata a tattauna cikin natsuwa tsakanin dalibai da hukumar gudanarwa ya rikide zuwa batun da ke ta yawo da shi kafafen yaɗa labarai, abin da ta ce ya rage martabar jami’ar a idon jama’a.

Advertisement

Cigaban MAAUN Akai-Akai Ya Sauya Matakin Jami’o’i Masu Zaman Kansu A Najeriya

Fateemah ta nuna rashin amincewarta da yadda wasu ɗalibai suka kai korafi ga hukumomi da kafofin watsa labarai maimakon su tattauna kai tsaye da jami’ar.

Ta kuma kalubalanci matakin Hukumar Yaki da Cin Hanci da Kare Haƙƙin Jama’a (PCACC) na umartar jami’ar da ta dakatar da karɓar kudin yaye dalibai, tana mai kiran hakan take hakkin jama’ar nr da ke da ikon tsara kudaden gudanarwarta.

Advertisement

A cewarta, wani gidan jaridar yanar gizo—Solacebase—na wallafa rahotanni a kan MAAUN ta wata siga da ta ce tana kama da ƙoƙarin rage martabar jami’ar.

Ta yi zargin cewa wannan ba shi ne karon farko da shafin ya yi irin wannan ba, duk kuwa da cewa jami’ar ta samu nasarori da dama, ciki har da matsayinta a AD Scientific Index, wanda ke nuna ci gaban ta a fannin bincike da koyarwa.

Advertisement

Fateemah ta ce a cikin kwanaki kaɗan za ta karɓi kyautar Campus Journalism Award, amma irin waɗannan nasarorin ba sa samun irin kulawar da ake bai wa rahotannin da suka kunshi ce-ce-ku-ce game da jami’ar.

Rubutun ya kuma yi magana kan ɗaya daga cikin waɗanda suka yi zanga-zangar, wanda ta zarga da rashin ɗabi’a, tana mai cewa ya yi kunar bakin wake a kafafen sada zumunta har da zagi ga shugaban jami’ar.

Advertisement

Ta ce irin wannan hali bai dace da ɗalibin da ake sa ran zai karɓi digiri bisa ka’idar “koyon ilimi da ladabi” ba.

A cewar Fateemah, kashi 85% na daliban da za su yi yaye sun riga sun biya kudin, inda wasu daga cikin masu sukar lamarin ma ba cikin jerin waɗanda za su kammala karatu suke ba.

Advertisement

Ta ce akwai rahotanni na yadda aka bude shafukan sada zumunta da sunan jami’ar tare da amfani da tambararta—ba tare da izinin hukumarta ba—abin da ta ce na iya jefa martabar jami’ar cikin haɗari.

A ƙarshe, ta yi addu’ar ganin jami’ar ta ci gaba da bunƙasa, tana mai fatan za ta shiga jerin fitattun cibiyoyin ilimi a nahiyar Afirka da ma duniya gaba ɗaya.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending