News
Shugaban NUJ Na Ƙasa Ya Jagoranci Buɗe Ofishin Kano Online Media Chapel, Yayi Alƙawarin Inganta Walwalar Ƴan Jarida
Shugaban Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya, ya yabawa Majalisar NUJ ta Jihar Kano bisa sabbin tsare-tsare, jagoranci mai haɗa kai da kuma shirye-shiryen da ke ƙarfafa haɗin kan mambobin ƙungiyar.
Ya bayyana hakan ne a yayin liyafar rufe bikin Makon ’Yan Jarida na NUJ na shekarar 2025 da NUJ ta Kano ta shirya a ranar Asabar a Cibiyar ’Yan Jarida (Press Centre) da ke Kano, inda aka kuma buɗe ofishin Kano Online Media Chapel.
Kwamared Yahaya ya ce Majalisar NUJ ta Kano na daga cikin majalisun da yake alfahari da su, yana mai yabawa shugabanni a matakai daban-daban bisa jajircewa, haɗin kai da tsayayyiyar manufa wajen bunƙasa aikin jarida.
Shugaban NUJ na ƙasa ya kuma yabawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa ƙwazo da jajircewa wajen tallafa wa fannin yaɗa labarai. A cewarsa, zuba jarin da gwamnatin jihar ke yi ya taimaka wajen ƙarfafa aikin jarida da bunƙasa ƙwarewar ’yan jarida.
Yayin da ake tunkarar shekarar 2026, Kwamared Yahaya ya yi kira ga ’yan jarida da su rungumi ƙwarewa, gaskiya da ɗabi’a, tare da zama jakadu nagari ta hanyar kare martabar aikin jarida da saita ajandar da za ta amfanar da al’umma.
Ya kuma bayyana cewa shugabancin NUJ na ƙasa na tattaunawa da Ma’aikatar Yaɗa Labarai domin inganta albashi da walwalar ’yan jarida a kafafen yaɗa labarai na tarayya, yana mai cewa idan aka aiwatar da hakan, ƙungiyar za ta nemi a faɗaɗa shirin zuwa jihohi 36 na ƙasar.
Haka kuma, ya sanar da shirin ƙaddamar da tsarin inshorar lafiya ga ’yan jarida, wanda zai rage nauyin kuɗin jinya, taimakawa lafiyar mata masu juna biyu da kuma tallafa wa burin samar da inshorar lafiya ga kowa.
A nasa jawabin, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kuduri aniyar inganta walwala da ƙwarewar ’yan jarida.
Ya ambaci shirye-shiryen ƙara wa ’yan jarida ƙwarewa, samar da manufofin yaɗa labarai na jihar, shigar da kafafen intanet cikin tsarin aiki, da kuma kafa ƙungiyar tsofaffin ’yan jarida domin tallafa musu da jagorantar matasa.
A nasa ɓangaren, Shugaban Kano Online Media Chapel, Abubakar Abdulkadir Dangambo, ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin jihar, shugabancin NUJ na ƙasa da na jihar Kano bisa rawar da suka taka wajen kafuwa da amincewa da sabon chapel ɗin.
Dangambo ya tabbatar da cewa Kano Online Media Chapel zai ci gaba da aiki bisa ƙa’idojin aikin jarida, tare da kare mutunci da martabar Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya.
