Connect with us

News

Kuskuren Harin Sojin Sama Ya Sake Hallaka Fararen Hula A Borno

Published

on

Wani Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Hallaka Mutane Da Dama A Sokoto 

Rahotanni daga jihar Borno na nuni da cewa hare-hare dakarun Sojin Sama da suka nufaci kaiwa kan ƴan ta’addan da ke ɓoye a yankin ya kai ga kisan ɗimbin fararen hula.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an kai hare-haren ne a ranar 14 ga watan nan can a Mararraba da ke ƙaramar hukumar Kukawa.

Advertisement

Al’ummar Gari Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara

Jaridar ta ce sojojin sun yi kuskuren luguden wuta kan Masunta da direbobin motocin hayar da ke dakon kifi wanda ya sabbaba asarar ɗimbin rayuka.

Wasu mutane 3 ganau da suka tsira da rayukansu a harin, sun ce motoci aƙalla 10 hare-haren suka lalata sai dai babu cikakkun alƙaluma kan mutanen da suka rasa rayukansu kodayake da  dama da suka jikkata na karɓar kulawa a babban asibitin Munguno.

Advertisement

Bayanai sun ce tsawon sa’o’i sojin saman na Najeriya suka shafe suna luguden wutar wanda suka faro tun da ƙarfe 6 na asubahi har zuwa 4 na yammacin ranar Asabar 14 ga watan da muke na Disamba.

Wannan kuskuren hari na zuwa sa’o’i bayan rundunar Sojin saman Najeriyar ta sha alwashin baiwa jama’a kariya ta hanyar kakkaɓe barazanar ƴan ta’addan a sabon sumamen da ta faro da taimakon Amurka.

Advertisement

 

FRI HAUSA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending