News
Mutane 11 Sun Rasu, 9 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Jigawa
Aƙalla mutane 11 ne suka mutu, yayin da wasu 9 suka jikkata, sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a ƙauyen Beguwa, kan titin Sankara, a ƙaramar hukumar Ringim ta Jihar Jigawa, a arewacin Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa hatsarin na da alaƙa da ɗaukar fasinjoji fiye da kima, tare da zargin ganganci daga direban motar. Direban na daga cikin mutanen da suka samu raunuka, kuma yana karɓar magani a wani asibiti.
Baffa Babba Dan Agundi Ya Taya Ganduje Murnar Cika Shekaru 76
Kakakin rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, SP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce da zarar direban ya murmure, za a miƙa shi zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) domin ci gaba da bincike.
“Da zarar direban ya samu sauƙi, za mu miƙa shi SCID domin tuhumarsa da kashe mutane ta hanyar ganganci,” in ji kakakin ’yan sandan.
Rundunar ’yan sandan ta jaddada kira ga direbobi da su mutunta dokokin hanya da gujewa lodin da ya wuce ƙa’ida, domin rage yawaitar hatsarurrukan mota a jihar.
