News
Akalla Mutane 26,866 Suka Kamu Da Cutar Ƙyanda, Yayin Da Mutane 153 Suka Rasu – NCDC
Hukumar Kula da Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) ta bayyana cewa akalla ’yan Najeriya 26,866 ne suka kamu da cutar ƙyanda, yayin da mutane 153 suka rasu daga watan Janairu zuwa Nuwambar shekarar 2025.
Wannan na ƙunshe ne a cikin rahoton cutar ƙyanda na watan Nuwamba 2025 da hukumar ta fitar, inda ta nuna cewa ba a samu asarar rai ba a watan Nuwamba, duk da samun rahotannin ɓarkewar cutar a wasu sassan ƙasar, musamman a tsakanin yaran da ba a yi wa rigakafi ba.
Ana Hasashen Gwamnan Kano Zai Koma APC, Murta Sule-Garo Na Iya Zama Mataimakin Gwamna
NCDC ta ce an samu mutane 71 da ake zargin sun kamu da ƙyanda a watan Nuwamba a jihohi 20 da kuma ƙananan hukumomi 47.
Daga cikin waɗannan rahotanni, guda ɗaya kacal (1.41%) aka tabbatar da kamuwa da cutar ta gwajin ɗakin gwaje-gwaje, yayin da mutane 63 (88.7%) ba a bayyana sakamakon gwajinsu ba. An kuma yi watsi da rahotannin mutane bakwai bayan bincike.
Jihohin da aka fi samun rahoton kamuwa da cutar sun haɗa da Delta (13), Kwara (6), Bayelsa (6), Jigawa (6) da Akwa Ibom (5), waɗanda gabaɗaya suka kai kaso 50.7% na dukkan rahotannin watan.
Hukumar ta jaddada cewa ba a tabbatar da mutuwar kowa ba daga cikin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar a watan Nuwamba.
Daga Janairu zuwa Nuwamba 2025, NCDC ta ce dukkan jihohi 36 na Najeriya, ciki har da Abuja, sun fuskanci rahotannin kamuwa da ƙyanda, lamarin da ya shafi ƙananan hukumomi 507.
Jihohin da abin ya fi shafa su ne Borno (7,968), Zamfara (4,779), Yobe (2,076), Bauchi (1,574) da Kebbi (1,357)—adadin da ya kai kaso 66.1% na jimillar waɗanda aka samu da cutar a ƙasar.
Daga cikin mutane 26,866 da aka samu:
19,213 (71.5%) an tabbatar sun kamu da cutar,
2,791 an tabbatar da kamuwa da su ta gwajin ɗakin gwaje-gwaje,
6,440 (23.8%) an yi watsi da rahotanninsu,
1,213 (3.4%) kuma bincike na ci gaba a kansu.
Yara da matsalar rigakafi
Rahoton NCDC ya nuna cewa yara masu shekaru 9 zuwa watanni 59 su 9,399 aka tabbatar sun kamu da ƙyanda, wato kaso 48.9%.
Hukumar ta bayyana cewa akwai babbar giɓi a rigakafin ƙyanda, inda kaso 77% (14,801) na waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar ba su taɓa karɓar allurar rigakafi ba.
A dunkule, mutane 153 ne suka mutu daga cikin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar a wannan lokaci, wanda ya kai kaso 0.8%, adadin da ya yi daidai da abin da aka samu a shekarar 2024.
NCDC ta ce an samu ɓarkewar cutar ƙyanda a ƙananan hukumomi 188 na jihohi 27 tsakanin Janairu da Nuwamba 2025.
Sai dai zuwa ƙarshen watan Nuwamba, hukumar ta ce ɓarkewar cutar ta tsaya a ƙananan hukumomi 187, inda ƙaramar hukumar Eti Osa a jihar Legas kaɗai ta rage da rahoton ci gaba da kamuwa da cutar. Ba a samu sabon ɓarke wa ba a watan.
Hukumar ta jaddada buƙatar ƙara faɗaɗa allurar rigakafi, sa ido da kai ɗauki cikin gaggawa, domin hana sake ɓarkewar cutar, musamman a tsakanin yara.
Ƙyanda cuta ce mai saurin yaɗuwa wadda ƙwayar cuta ke haddasawa. Yawanci takan fi kama yara da ba a yi wa rigakafi ba, sai dai manya ma na iya kamuwa da ita.
Cutar takan fara ne da zazzaɓi, tari, mura, hawaye ko jajayen ido, kafin daga bisani ƙuraje su bayyana a jiki. Idan ta tsananta, ƙyanda na iya haddasa numoniya, gudawa, makanta, ko ma rasa rai, musamman ga ƙananan yara da masu raunin garkuwar jiki.
Ƙyanda na yaɗuwa cikin sauƙi ta iska, musamman idan mai cutar ya yi tari ko atishawa. Masana lafiya na jaddada cewa rigakafi ita ce hanya mafi inganci ta kare kai daga kamuwa da cutar
