News
Jami’an NDLEA Sun Cafke Masu Safarar Ƙwayoyi Bisa Yunkurin Fitar Da Hodar Iblis Zuwa Birtaniya
Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) sun kama wani mutum mai suna Chidiebere Basil, mai shekaru 37, tare da wasu mutane uku, bisa zargin yunƙurin fitar da hodar iblis zuwa ƙasar Birtaniya ta filin jirgin sama.
A wata sanarwa da kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce jami’an NDLEA sun gano buhuna 75 na hodar iblis, masu nauyin kilogiram 1.50, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
Akalla Mutane 26,866 Suka Kamu Da Cutar Ƙyanda, Yayin Da Mutane 153 Suka Rasu – NCDC
Babafemi ya bayyana cewa an fara kama mutane uku — Jubrin, Kuku Daniel Oluwasegun da Igwe Chioma — a ranar 20 ga Disamba, kafin daga bisani bincike ya kai ga gano Basil a matsayin jagoran wannan tawaga.
Ya ce an cafke Basil ne a wani wurin shakatawa da ke Ikeja, bayan bayanan da aka samu daga waɗanda aka kama tun da farko.
Sanarwar ta ce Basil tsohon sanannen ɗan safarar miyagun ƙwayoyi ne, inda a baya aka kama shi da laifin safarar kilogiram 30.10 na ƙwayoyi a watan Mayun 2023, yayin da yake ƙoƙarin tafiya zuwa Landan.
A wancan lokaci, an gurfanar da shi a gaban kotu, inda aka same shi da laifi, aka kuma yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari, tare da zaɓin biyan tarar kuɗi.
Hukumar NDLEA ta ce bayan kammala binciken da ake yi, za ta ɗauki matakan shari’a da suka dace kan dukkan waɗanda abin ya shafa.
