Connect with us

News

“A Siyasa Babu Abota Ko Gaba Ta Har Abada” — Farfesa Kamilu Sani Fagge

Published

on

241447654 10159709030848035 819184409727171553 n

Masanin kimiyyar siyasa a Najeriya, Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya ce siyasa ba ta tafiya da jin daɗi ko ɗaure kai ga mutum ko ƙungiya na dindindin. A cewarsa, siyasa ra’ayi ce da maslaha ke jagoranta, inda matsayi ke sauyawa gwargwadon yanayi da bukatun lokaci.

Farfesan ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan yadda ake yawan sauya sheƙa da kulla kawance a fagen siyasar Najeriya.

Advertisement

Jigo a Jamiyyar APC ta Adamawa ya bukaci matasa da su rungumi zaman lafiya dan samun cigaba

Ya ce “babu aboki na dindindin, babu maƙiyi na dindindin, haka kuma babu jin kunya ta dindindin a siyasa,” yana mai nuni da cewa sauyin matsayi wani bangare ne na tsarin siyasa.

A halin yanzu, jam’iyyun siyasa a ƙasar na fama da ƙalubale da dama da suka haɗa da rikice-rikicen cikin gida, sabani kan shugabanci,

Advertisement

A cewar masu sharhi, waɗannan matsaloli sun raunana tsari da akidar jam’iyyu, tare da ƙara yawaitar sauya sheƙa a tsakanin ’yan siyasa.

Wasu masana na ganin cewa rashin tsayayyen tsari da fifita muradin kai na daga cikin dalilan da ke haddasa wannan yanayi.

Advertisement

A lokuta da dama, ’yan siyasa na duba inda za su samu damar cin zaɓe ko kusanci da madafun iko, fiye da tsayawa kan manufofin jam’iyyarsu.

Farfesa Fagge ya ce jam’iyyun adawa na fuskantar matsalar rabuwar kai, yayin da jam’iyyar da ke kan mulki ke ƙoƙarin daidaita ra’ayoyi masu karo da juna a cikinta.

Advertisement

A cewarsa, wannan yanayi na haifar da siyasa mai dogaro da kawance na wucin-gadi, ba tare da gina tubalin dimokuraɗiyya mai ƙarfi ba.

Wannan tsokaci na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan makomar jam’iyyun siyasa da yiwuwar sauyin kawance gabanin manyan zaɓukan da ke tafe a Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending