Connect with us

News

Dakarun Sojin Sama Sun Yi Nasarar Hallaka Ƴan Ta’adda Dubu 2 Da 351 A 2025

Published

on

Wani Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Hallaka Mutane Da Dama A Sokoto 
Spread the love

Rundunar Sojin saman Najeriyar ta bayyana shekarar da ta gabata ta 2025 a matsayin mafi nasara a gareta a yaƙin da ta ke da ɓatagarin da suka addabi ƙasar, bayan da ta ce ta yi nasarar kakkaɓe ƴan ta’addan da yawansu ya kai dubu 2 da 351 a mabanbantan hare-haren da ta ke kaiwa maɓoyarsu a sassa daban-daban na ƙasar.

Cikin wata sanarwa da ta fitar ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar Air Commodore Ehimen Ejodame ta bayyana cewa Sojin saman na Najeriya, sun kai hare-hare har sau 379 kan maɓoyar ƴan ta’addan daban-daban ciki har da hare-hare 274 ta sama kaɗai wanda ya ƙunshi farmakar sashen tattara bayanansu da tsaren kai hare-hare sai kuma inda suke atisaye da ma inda suke ɓoyen makamansu.

Muhimman Abubuwan Da Suka Faru A 2025 A  Najeriya ‎

Sanarwar ta rundunar Sojin Najeriya ta ce a tsawon shekarar ta 2025 dakarunsu sun shafe tsawon sa’o’in da suka kai 800 suna shawagi da jirage a sararin samaniya wajen kai hare-haren tare da kisan tarin ɓatagarin.

 

Advertisement

A sanadiyyar wannan hare-hare rundunar Sojin saman ta ce an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankuna da dama da a baya ke fuskantar barazanar ƴan ta’adda.

A cewar sanarwar hare-haren sun faru a yankunan Arewa maso gabashi da kuma Arewa maso yammaci baya ga tsakiyar Najeriyar, yankunan da dukkaninsu ke fama da matsalolin tsaro daga mabanbantan ƴan ta’adda da tsagerun da ke hana jama’a sakat.

Tun bayan da Amurka ta yiwa Najeriya barazanar ɗaukar matakin Soji don fansar kisan Kiristocin da ta yi zargin ana yi a sassan ƙasar, Sojin Najeriyar suka matsa ƙaimi wajen kai hare-hare kan ɓatagarin wanda aka ga lafawarsu daga watan Nuwamban na 2025 kawo yanzu.

Matsalolin tsaro masu alaƙa da mayaƙan ƴan ta’adda masu iƙirarin jihadi da kuma ƴan bindigar da ke satar mutane don neman fansa baya ga masu kisan babu gaira babu dalili sun yi Najeriyar katutu a kusan dukkanin yankunan arewacin ƙasar kodayake an fi ganin ta’azzarar matsalar a jihohin Zamfara da Kebbi da Sokoto da Neja da Kaduna da kuma jihar Borno da ke matsayin cibiyar Boko Haram.

Advertisement

 

RFI

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *