Connect with us

News

Dubu 100 Aka Biya Ni Na Sanya Bam A Masallaci Da Ke Maiduguri — Ɗan Ƙunar Baƙin 

Published

on

IMG 20251231 134545
Spread the love

Wani matashi da ake zargin ɗan Boko Haram ne, Ibrahim Mohammed, ya amsa cewa an biya shi Naira 100,000 domin kai harin bam a wani masallaci da ke Maiduguri, Jihar Borno.

Masani kan harkar tsaro, Zagazola Makama ne, ya bayyana hakan a ranar Laraba.

“A Siyasa Babu Abota Ko Gaba Ta Har Abada” — Farfesa Kamilu Sani Fagge

Ya ce sojojin Operation Hadin Kai tare da taimakon mafarauta ne sun kama Ibrahim a Damaturu, a Jihar Yobe.

Makama ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa yana da hannu a harin bam da aka kai a Masallacin Gamboru Market a ranar 24 ga watan Disamba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu 32.

Advertisement

“Sunana Ibrahim daga Michika a Jihar Adamawa. Shugabanninmu ne suka aike mu Maiduguri domin dasa bam a Masallacin Izala,” in ji shi.

Ibrahim ya bayyana cewa sun dasa bam ɗin ne lokacin da babu jama’a a masallacin, sannan suka saita shi ya fashe a lokacin sallar Magariba.

“Ana biyana tsakanin Naira 70,000 zuwa Naira 100,000 kan kowane aiki.

“Bayan fashewar bam ɗin ma, na dawo na yi kamar ina taimakawa wajen ɗaukar waɗanda suka jikkata,” in ji shi.

Advertisement

Hukumomin tsaro sun ce Ibrahim na cikin wata babbar ƙungiyar ‘yan ta’adda da ke shirin kai hare-hare a yankin Arewa maso Gabas.

Sun kuma yi gargaɗin cewa ana zargin ya bar wata jaka mai ɗauke da bam a kusa da wani masallaci a Maiduguri, wadda har yanzu ba a gano ta ba.

 

LEADSHIP HAUSA 

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *