News
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Garin Maƙarfi A Jihar Kaduna
Rahotanni da ke shigowa Jaridar Inda Ranka sun nuna cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari a garin Maƙarfi da ke Jihar Kaduna a daren yau.
Majiyoyi daga cikin mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun shiga garin ne cikin dare, inda suka fara harbe-harbe da bindigogi wanda ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da tashin hankali.
Mojtaba Khamenei Ya Gaji Mahaifinsa A Matsayin Jagoran Addinin Iran
Mazauna garin sun ce ana ci gaba da jin ƙarar harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya sa mutane da dama suka shiga gidajensu domin neman mafaka.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu cikakken bayani kan ko akwai asarar rayuka ko dukiyoyi sakamakon harin.
Haka kuma ba a samu wata sanarwa daga jami’an tsaro ba dangane da lamarin.
Advertisements
