News
RIKICIN GABAS TA TSAKIYA: Farashin Litar Man Fetur Na Iya Kaiwa Naira 2000
Ƙungiyar masu gidajen mai a Najeriya ta yi gargadin cewa farashin litar man fetur na iya kai wa naira 2000, a yayin da diesel na iya tashi zuwa naira 3000 akan kowace lita idan har rikicin Iran da Amurka da Isra’ila a Gabas ta Tsakiya ya cigaba.
Shugaban ƙungiyar Billy Gillis-Harry ne ya yi wannan gargaɗi a lokacin da yake gabatar da jawabi a Port Harcourt.
Ya ce cigaba da tashin farashin makamashi na iya ta’azzara hauhawar farashin kayayyaki, haddasa rashin ayyukan yi ya kuma munana matsin tattalin arziki,ya kuma sa kuɗin sufuri ya yi tashin gwauron zabi a faɗin ƙasar.
A cewar sa, gabanin rikicin Gabas ta Tsakiya da ake yi a halin yanzu, ana sayar da litar man fetur akan naira 774, amma yanzu ya zarce naira dubu guda, wato an samu ƙarin kashi 30 kenan.
Zalika, man diesel, wanda kafin yanzu bai wuce naira 950 ba yanzu ya kai naira 1400, wato an samu ƙarin kashi 49.
Gillis-Harry ya buƙaci kamfanin NNPC na Najeriya da ya bada ƙarfi wajen tace ɗanyen mai a cikin gida a matsayin wani mataki na kare ƙasar daga matsalar ƙarancin mai da ta addabi duniya, inda ya buƙaci shugaban kamfanin Bayo Ojulari da ya tabbatar da dawo da aaikin tace ɗanyen mai a matatun man gwamnatin ƙasar.
