Connect with us

News

An Ƙara Farashin Ruwan ‘Pure Water’ A Kano 

Published

on

pjimage 2
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Ƙungiyar masu samar da ruwan leda, wato pure water, a jihar Kano ta sanar da ƙarin farashin ruwan a faɗin jihar.

Ƙungiyar ta ce matakin ya biyo bayan hauhawar farashin kayan da ake amfani da su wajen samar da ruwan, lamarin da ya jefa masana’antar cikin mawuyacin hali.

Duk Wanda Ke Tunanin Zai Iya Rusa Iran Bai San Tarihi Ba —Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar, Anas Idris Hassan, ya fitar, ya bayyana cewa ƙarin farashin wani mataki ne da suka ɗauka domin tabbatar da ci gaba da samar da ruwan sha mai tsafta ga al’umma.

Sanarwar ta ce farashin buhun ruwan leda wanda a baya ake sayarwa kan Naira 220, yanzu an ƙara shi zuwa akalla Naira 300.

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa ƙarin farashin ya zama dole domin guje wa durƙushewar masana’antar, musamman ganin yadda farashin kayan aiki da makamashi ke ci gaba da tashi a ƙasar nan.

Advertisement

 

 

NIGERIAN TRACKER 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending