Connect with us

News

Matatar Dangote  Ta Ƙara Farashin Man Fetur Zuwa N1,245 Kan Kowace Lita

Published

on

Matatar Man Dangote ta zargi hukumar NUPRC da gazawa wurin gudanar da ayyukanta

Matatar Dangote  ta sanar da ƙarin farashin man fetur daga N1,175 zuwa N1,245 kan kowace lita, matakin da ake sa ran zai ƙara tsadar mai a gidajen mai a fadin Najeriya.

Kamfanin ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya aikewa dillalan mai a daren Juma’a, inda ya danganta ƙarin farashin da tsanantar rikice-rikicen siyasa a duniya, musamman a yankunan da ake hako ɗanyen mai.

Advertisement

Nan Ba Da Jimawa Ba Za A Biya Diyya Ga Mafarautan Kano Da Aka Kashe A Edo — Gwamnatin Kano

A cewar matatar, sabon farashin zai fara aiki daga tsakar daren ranar 21 ga Maris, 2026, kuma zai shafi dukkan man da ba a ɗauka ba daga matatar .

Advertisement

Masana sun ce wannan sauyi na nuna yadda kasuwar man fetur a Najeriya ke ci gaba da fuskantar tasirin canjin farashin ɗanyen mai a duniya da kuma matsalolin sufuri, duk da fara aiki da matatar Dangote wadda aka yi fatan za ta taimaka wajen daidaita samar da mai a cikin gida.

Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar rashin tabbas a kasuwar mai ta duniya, sakamakon rikice-rikice a yankunan Gabas ta Tsakiya, wanda ke haddasa tashin farashin ɗanyen mai da kuma ƙarin kuɗin jigilar kayayyaki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending