News
KANO: Kwamitin Binciken KNUPDA Ya Buɗe Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe Da Shawarwarin Jama’a
Kwamitin Bincike kan Ayyukan Hukumar Tsarawa da Raya Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) ya gayyaci al’ummar jihar da sauran masu ruwa da tsaki da su gabatar da ƙorafe-ƙorafe da takardun shawarwari domin taimakawa binciken da yake gudanarwa kan ayyukan hukumar.
A wata muhimmiyar sanarwa da kwamitin ya fitar, ya ce ana buƙatar jama’a su miƙa rubutattun ƙorafe-ƙorafe kan yadda KNUPDA ke gudanar da ayyukanta, musamman waɗanda suka shafi bayar da lasisin gine-gine, amincewa da tsare-tsaren gine-gine, kula da ci gaban gine-gine da kuma aiwatar da dokoki da ƙa’idojin tsara birane.
Gwamnatin Kano Ta Ƙaddamar Da Sabon Shirin Wayar Da Kan Matasa Kan Rajistar Zaɓe
Kwamitin ya bayyana cewa yana son karɓar bayanai daga jama’a kan yiwuwar samun jinkiri wajen bayar da izinin gine-gine da na bunƙasa muhalli, amincewa da amfani da filaye, da kuma matakan tilasta bin doka da sashen kula da gine-gine ke ɗauka.

Sanarwar ta ce duk masu son gabatar da ƙorafi ko shawarwari su aika da su ga Shugaban Kwamitin Bincike kan Ayyukan KNUPDA, Dr. Dalhatu Aliyu Sani, tare da rubuta cikakken sunansu, lambar waya da adireshinsu, sannan su bayyana korafinsu cikin gamsasshen bayani.
Haka kuma, kwamitin ya buƙaci masu ƙorafi su haɗa da duk wasu hujjoji ko takardun da za su tabbatar da zarge-zargen ko bayanan da suka gabatar.
An ce za a karɓi dukkan ƙorafe-ƙorafe da takardun shawarwari ne a hedikwatar KNUPDA da ke Titin Durbin Katsina, Bompai, a Kano.
Kwamitin ya sanya ranar 1 ga Yulin 2026 a matsayin wa’adin rufe karɓar ƙorafe-ƙorafe da takardun shawarwari.
Sai dai ya yi gargaɗin cewa duk bayanan da za a gabatar dole ne su kasance na gaskiya, masu inganci kuma an gabatar da su cikin kyakkyawar niyya, yana mai jaddada cewa yana da cikakken ikon tantance sahihancin duk bayanan da aka miƙa masa.
Kwamitin ya bayyana cewa matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin tabbatar da gaskiya, riƙon amana da inganta ayyukan tsara da raya birane a Jihar Kano.
